التصنيفات
القرآن الكريم

Surah At-Tahrim ( The Prohibition ) [12]

وَمَرْيَمَ ابْنَتَ عِمْرَانَ الَّتِي أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتْ بِكَلِمَاتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِ وَكَانَتْ مِنَ الْقَانِتِينَ ( 12 ) 

Da Maryama ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli’u.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Mu’minoon ( The Believers ) [50]

وَجَعَلْنَا ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ آيَةً وَآوَيْنَاهُمَا إِلَىٰ رَبْوَةٍ ذَاتِ قَرَارٍ وَمَعِينٍ ( 50 ) 

Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma’abũcin natsuwa da marẽmari.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Anbiya ( The Prophets ) [91]

وَالَّتِي أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلْنَاهَا وَابْنَهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ ( 91 ) 

Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Maryam ( Mary ) [16-35]

وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مَرْيَمَ إِذِ انتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًا شَرْقِيًّا ( 16 ) 

Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.

فَاتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَابًا فَأَرْسَلْنَا إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرًا سَوِيًّا ( 17 ) 

Sa’an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.

قَالَتْ إِنِّي أَعُوذُ بِالرَّحْمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيًّا ( 18 ) 

Ta ce: “Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!”

قَالَ إِنَّمَا أَنَا رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَامًا زَكِيًّا ( 19 ) 

Ya ce: “Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki.”

قَالَتْ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَرٌ وَلَمْ أَكُ بَغِيًّا ( 20 ) 

Ta ce: “A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?”

قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ ۖ وَلِنَجْعَلَهُ آيَةً لِّلنَّاسِ وَرَحْمَةً مِّنَّا ۚ وَكَانَ أَمْرًا مَّقْضِيًّا ( 21 ) 

Ya ce: “Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.’ Kuma abin yã kasance wani al’amari hukuntacce.”

فَحَمَلَتْهُ فَانتَبَذَتْ بِهِ مَكَانًا قَصِيًّا ( 22 ) 

Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.

فَأَجَاءَهَا الْمَخَاضُ إِلَىٰ جِذْعِ النَّخْلَةِ قَالَتْ يَا لَيْتَنِي مِتُّ قَبْلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسْيًا مَّنسِيًّا ( 23 ) 

Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce “Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!”

فَنَادَاهَا مِن تَحْتِهَا أَلَّا تَحْزَنِي قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيًّا ( 24 ) 

Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, “Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.

وَهُزِّي إِلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تُسَاقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًا جَنِيًّا ( 25 ) 

“Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã ‘ya’yan dabĩno, ruɗabi nunannu.”

فَكُلِي وَاشْرَبِي وَقَرِّي عَيْنًا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ الْبَشَرِ أَحَدًا فَقُولِي إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمَٰنِ صَوْمًا فَلَنْ أُكَلِّمَ الْيَوْمَ إِنسِيًّا ( 26 ) 

“Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, ‘Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba.”

فَأَتَتْ بِهِ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُ ۖ قَالُوا يَا مَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْئًا فَرِيًّا ( 27 ) 

Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: “Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!

يَا أُخْتَ هَارُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ امْرَأَ سَوْءٍ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيًّا ( 28 ) 

“Yã ‘yar’uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba.”

فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ ۖ قَالُوا كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي الْمَهْدِ صَبِيًّا ( 29 ) 

Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: “Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?”

قَالَ إِنِّي عَبْدُ اللَّهِ آتَانِيَ الْكِتَابَ وَجَعَلَنِي نَبِيًّا ( 30 ) 

Ya ce: “Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi.”

وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَانِي بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيًّا ( 31 ) 

“Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai.”

وَبَرًّا بِوَالِدَتِي وَلَمْ يَجْعَلْنِي جَبَّارًا شَقِيًّا ( 32 ) 

“Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri.”

وَالسَّلَامُ عَلَيَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّا ( 33 ) 

“Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai.”

ذَٰلِكَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ ۚ قَوْلَ الْحَقِّ الَّذِي فِيهِ يَمْتَرُونَ ( 34 ) 

Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.

مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍ ۖ سُبْحَانَهُ ۚ إِذَا قَضَىٰ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ ( 35 ) 

Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce masa, “Kasance.” Sai ya dinga kasan cẽwa.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) [116]

وَإِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيْنِ مِن دُونِ اللَّهِ ۖ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ ۚ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ ۚ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلَا أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ ۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ ( 116 ) 

Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: “Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, ‘Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?” (Ĩsã) Ya ce: “Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne.”

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) [110]

إِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ اذْكُرْ نِعْمَتِي عَلَيْكَ وَعَلَىٰ وَالِدَتِكَ إِذْ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ الْقُدُسِ تُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ وَكَهْلًا ۖ وَإِذْ عَلَّمْتُكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ وَالْإِنجِيلَ ۖ وَإِذْ تَخْلُقُ مِنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ بِإِذْنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيْرًا بِإِذْنِي ۖ وَتُبْرِئُ الْأَكْمَهَ وَالْأَبْرَصَ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ تُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ كَفَفْتُ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَنكَ إِذْ جِئْتَهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ ( 110 ) 

A lõkacin da Allah Ya ce: “Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni’ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa’an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã’ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: ‘Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.’

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) [75]

مَّا الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ وَأُمُّهُ صِدِّيقَةٌ ۖ كَانَا يَأْكُلَانِ الطَّعَامَ ۗ انظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ الْآيَاتِ ثُمَّ انظُرْ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ ( 75 ) 

Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa’an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) [17]

لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ ۚ قُلْ فَمَن يَمْلِكُ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا إِنْ أَرَادَ أَن يُهْلِكَ الْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ۗ وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ( 17 ) 

Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: “Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama,” sun kãfirta. Ka ce: “To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?” Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah An-Nisa ( The Women ) [171]

يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ وَلَا تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ ۚ إِنَّمَا الْمَسِيحُ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ رَسُولُ اللَّهِ وَكَلِمَتُهُ أَلْقَاهَا إِلَىٰ مَرْيَمَ وَرُوحٌ مِّنْهُ ۖ فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ ۖ وَلَا تَقُولُوا ثَلَاثَةٌ ۚ انتَهُوا خَيْرًا لَّكُمْ ۚ إِنَّمَا اللَّهُ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۖ سُبْحَانَهُ أَن يَكُونَ لَهُ وَلَدٌ ۘ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا ( 171 ) 

Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, “Uku”. Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.

التصنيفات
القرآن الكريم

Surah An-Nisa ( The Women ) [156]

وَبِكُفْرِهِمْ وَقَوْلِهِمْ عَلَىٰ مَرْيَمَ بُهْتَانًا عَظِيمًا ( 156 ) 

Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.