عربيEnglish

The Noble Qur'an Encyclopedia

Towards providing reliable exegeses and translations of the meanings of the Noble Qur'an in the world languages

The Table Spread [Al-Maeda] - Hausa translation - Abu Bakr Jomy - Ayah 12

Surah The Table Spread [Al-Maeda] Ayah 120 Location Madanah Number 5

۞ وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ لَئِنۡ أَقَمۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيۡتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرۡتُمُوهُمۡ وَأَقۡرَضۡتُمُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ فَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ [١٢]

Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu* daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩ Na, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."