التصنيفات
القرآن الكريم

المختصر في التفسير Hausa سورة [آل عمران]

۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰٓ ءَادَمَ وَنُوحٗا وَءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ وَءَالَ عِمۡرَٰنَ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

الهوساوية | Hausa

Haqiqa Allah ya zavi Annabi Adam (عليه السلام) ya sanya malaikunsa suka yi masa sujjada. Ya zavi Annabi Nuhu, ya sanya shi farkon Manzo zuwa ga mutanen da suke bayan qasa. Ya zavi iyalan Annabi Ibrahim ya sanya annabci ya wanzu a cikin zuriyarsa. Ya zavi iyalan Imrana. Dukkan waxannan ya zave su, ya fifita su a kan mutanen zamaninsu.

ذُرِّيَّةَۢ بَعۡضُهَا مِنۢ بَعۡضٖۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

الهوساوية | Hausa

Waxannan da aka ambata daga annabawa da zuriyarsu, waxanda suka bi hanyarsu, to zuriya ce da sashenta daga sashe yake, a wajen kaxaita Allah da ayyuka nagari, suna gadon karamci da kyawawan halaye daga junansu. Allah yana jin maganganun bayinsa, kuma ya san ayyukansu, don haka ya zavi waxanda ya ga dama daga cikinsu, ya fifita waxanda ya ga dama daga cikinsu.

إِذۡ قَالَتِ ٱمۡرَأَتُ عِمۡرَٰنَ رَبِّ إِنِّي نَذَرۡتُ لَكَ مَا فِي بَطۡنِي مُحَرَّرٗا فَتَقَبَّلۡ مِنِّيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

الهوساوية | Hausa

Ka tuna – ya kai wannan Manzo – yayin da matar Imran, mahaifiyar nana Maryam (alaihas salam) ta ce: na Ubangiji ni na wajabta wa kaina zan sanya abin da yake cikin cikina ya zama naka kai kaxai, na yanta shi daga dukkan wata hidima, don ya yi maka hidima, ya yi wa xakinka hidima, ka karva daga gare ni. Haqiqa kai mai jin adduata ne, kuma masani ne ga niyyata.

فَلَمَّا وَضَعَتۡهَا قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي وَضَعۡتُهَآ أُنثَىٰ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا وَضَعَتۡ وَلَيۡسَ ٱلذَّكَرُ كَٱلۡأُنثَىٰۖ وَإِنِّيسَمَّيۡتُهَا مَرۡيَمَ وَإِنِّيٓ أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

الهوساوية | Hausa

Da cikinta ya kai ta haife abin da yake cikinta xin. Sai ta ce – tana mai bayar da uzuri, domin tana fatan cikin nata namiji ne – ta ce: ya Ubangiji na haife ta mace – Allah ya fi ta sanin abin da ta haifa – namijin da take fata ta samu ba kamar macen da aka ba ta yake ba, wajen qarfi da halitta. Na sa mata suna Maryam, kuma ina nema mata tsari da tsarinka tare da zuriyarta daga Shaixan, korarre daga rahamarka.

فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٖ وَأَنۢبَتَهَا نَبَاتًا حَسَنٗا وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّاۖ كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيۡهَا زَكَرِيَّا ٱلۡمِحۡرَابَ وَجَدَعِندَهَا رِزۡقٗاۖ قَالَ يَٰمَرۡيَمُ أَنَّىٰ لَكِ هَٰذَاۖ قَالَتۡ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٍ

الهوساوية | Hausa

Sai Allah ya karvi bakancenta kyakkyawar karva, ya rayar da ita a kyakkyawar tarbiyya, ya sanya zukatan mutanen qwarai daga cikin bayinsa suna tausayin ta. Ya sanya renonta a hannun Annabi Zakariyya (عليه السلام). Annabi Zakariyya ya kasance duk lokacin da ya shiga wurinta, inda take ibada, sai ya samu abinci mai daxi a wurinta. Sai ya yi mata magana ya ce mata: ya Maryam daga ina wannan abin arzikin yake? Sai ta ba shi amsa ta ce: wannan arzikin daga wajen Allah ne, haqiqa Allah yana azurta wanda ya ga dama arziki mai yalwa ba tare da lissafi ba.

وَإِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰكِ وَطَهَّرَكِ وَٱصۡطَفَىٰكِ عَلَىٰ نِسَآءِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

الهوساوية | Hausa

Ka tuna – ya kai wannan Manzo – yayin da malaiku suka cewa nana Maryam (Alaihas Salam): haqiqa Allah ya zave ki, saboda kin siffantu da kyawawan halaye. Ya tsarkake ki daga tawaya. Ya zave ki a kan matan talikai na zamaninki.

يَٰمَرۡيَمُ ٱقۡنُتِي لِرَبِّكِ وَٱسۡجُدِي وَٱرۡكَعِي مَعَ ٱلرَّـٰكِعِينَ

الهوساوية | Hausa

Ki yi doguwar tsayuwa a cikin sallah, ki yi sujjada ga Ubangijinki, ki yi rukui tare da masu rukuu daga cikin bayinsa salihai.

ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۚ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ يُلۡقُونَ أَقۡلَٰمَهُمۡ أَيُّهُمۡ يَكۡفُلُ مَرۡيَمَ وَمَا كُنتَلَدَيۡهِمۡ إِذۡ يَخۡتَصِمُونَ

الهوساوية | Hausa

Wannan abin da aka ambata na labarin Annabi Zakariyya da nana Maryam (Alaihas Salam) yana daga cikin labarukan gaibu da muke maka wahayinsu – ya kai wannan Manzo –. Ba ka tare da waxannan malaman da salihan bayin lokacin da suka yi jayayya a kan wanda ya fi cancanta ya xauki tarbiyyantar da nana Maryam, har sai da suka yi quria, suka jefa alqalumansu, sai alqalamin Zakariyya ya samu nasara.

إِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٖ مِّنۡهُ ٱسۡمُهُ ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ وَجِيهٗا فِيٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

الهوساوية | Hausa

Ya wannan Manzo ka tuna lokacin da malaiku suka ce: ya Maryam Allah yana miki albishir da yaro, wanda za a halitta ba da uba ba. Kawai za a halicce shi da kalmar Allah, da ya ce: kasance sai yaron ya kasance da izinin Allah. Sunan wannan yaron: Isa xan Maryam, yana da matsayi babba a duniya da lahira, kuma yana cikin makusanta ga Allah Maxaukakin Sarki.

وَيُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗا وَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

الهوساوية | Hausa

Zai yi wa mutane magana yana yaro qarami, tun kafin lokacin ya fara magana, kuma zai musu magana yana babba, a lokacin qarfinsa ya cika. Zai musu magana da abin da yake gyaruwar addininsu da rayuwarsu ne. Kuma yana cikin salihan mutane a cikin maganganunsu da ayyukansu.

قَالَتۡ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي وَلَدٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكِ ٱللَّهُ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَايَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

الهوساوية | Hausa

Maryam tana mai mamaki yaya za ta haifi xa ba tare da miji ba ta ce:ta yaya zai zama ina da xa alhali wani mutum bai tava kusanta ta ba, ta hanyar halal ko ta hanyar haram. Sai Malaika ya ce da ita, kamar yadda Allah ya halitta miki xa ba tare da uba ba, haka yake halittar abin da ya ga dama daga abubuwan da suka sava wa abin da aka sani na alada. Idan Allah ya yi nufin wani abu sai ya ce da shi: kasance sai ya kasance. Babu abin da yake gagarar sa.

وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

الهوساوية | Hausa

Zai koya masa rubutu da dacewa cikin magana da aiki. Kuma zai koya masa Attaura wadda ya saukar wa Annabi Musa (عليه السلام). Kuma ya koya masa Injila wadda zai saukar masa da ita.