وَبِكُفۡرِهِمۡ وَقَوۡلِهِمۡ عَلَىٰ مَرۡيَمَ بُهۡتَٰنًا عَظِيمٗا
الهوساوية | Hausa
Mun kore su daga rahama saboda kafircinsu, da sukan Maryamu alaihas salam da zina, don qarya da kage.
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَاٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا
الهوساوية | Hausa
Ya wannan Manzo ka ce wa Nasara, waxanda a ka ba wa Injila: “kada ku qetare iyaka a cikin addininku, kuma kada ku faxi komai a kan Annabi Isa (عليه السلام) ku dangana shi ga Allah sai dai gaskiya. Al-Masihu Isa xan Maryam Manzon Allah ne, Allah ya aiko shi da gaskiya, ya halicce shi da kalmarsa da ya aiko mala‘ika Jibrilu da ita zuwa ga Maryam, ita ce faxinsa “kun” wato “kasance” sai ya kasance, kuma ita ce busa daga Allah da mala‘ika Jibrilu ya yi busa da ita da umarnin Allah, don haka ku yi imani da Allah da Manzanninsa gaba xaya, ba tare da rarrabewa ba. Kada ku ce: abubuwan bauta guda uku ne. Ku bar wannan vatacciyar magana ta qarya, barin ta alheri gare ku a duniya da lahira. Allah ne kaxai abin bauta guda xaya, ya tsarkaka daga abokin tarayya, da xa, shi ne mawadaci, yana da mulkin sama da qasa, da mulkin abin da yake tsakaninsu. Kuma gwargwadon abin da yake cikin sama da qasa Allah ne mai kula da su da lura da su.