التصنيفات
القرآن الكريم

المختصر في التفسير Hausa سورة [المائدة]

لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ أَن يُهۡلِكَٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗاۗ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۚ يَخۡلُقُ مَايَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

الهوساوية | Hausa

Waxanda suke ce wa Al-Masihu Isa xan Maryam Allah ne sun kafirta. Ka faxa musu – ya kai wannan Manzo – waye yake da ikon ya hana Allah ya halakar da Al-Masihu Isa xan Maryam, kuma ya halakar da mahaifiyarsa, ya halakar da duk waxanda suke bayan qasa, idan ya yi nufin halaka su xin? Idan babu wanda zai iya hana shi aikata haka, to wannan ya nuna babu abin bautawa da cancanta da gaskiya sai Allah, kuma haqiqa kowa da kowa ; Isa xan Maryam, da Mahaifiyarsa, da sauran halitta, dukkaninsu halittar Allah ne. Allah ne yake da mulkin sammai da qassai da abin da yake tsakaninsu, yana halittar abin da ya ga dama, daga cikinsu akwai Isa xan Maryam, bawansa ne, Manzonsa ne. Kuma Allah mai iko ne a kan dukkan komai.

مَّا ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٞۖ كَانَا يَأۡكُلَانِ ٱلطَّعَامَۗ ٱنظُرۡكَيۡفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ ٱنظُرۡ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

الهوساوية | Hausa

Annabi Isa Almasihu xan Maryam bai kasance ba, face Manzo daga cikin manzanni, duk abin da yake gudana a kansu na mutuwa, yana gudana a kansa. Mahaifiyarsa Maryam mai yawan gaskiya ce da gaskatawa, su biyun duka suna cin abinci, saboda buqatarsu gare shi, to ta yaya za su zama ababan bauta, alhali suna buqatar abinci! Ya wannan Manzo ka duba, duba na lura, irin yadda muke bayyana musu ayoyi masu nuna kaxaitaka, da nuna vacin abin da suke kai na wuce-gona-da- iri wajen dangana allantaka ga wanin Allah, kuma su duk da haka suna inkarin waxannan ayoyi. Sannan ka sake dubawa, duba na lura, ta yaya ake juyar da su ga barin gaskiya, duk da waxannan ayoyi bayyanannu da suke nuna kaxaitakar Allah.

إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱذۡكُرۡ نِعۡمَتِي عَلَيۡكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذۡ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَفِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗاۖ وَإِذۡ عَلَّمۡتُكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَۖ وَإِذۡ تَخۡلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِبِإِذۡنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِيۖ وَتُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡكَفَفۡتُ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَنكَ إِذۡ جِئۡتَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

الهوساوية | Hausa

Ka tuna lokaci da Allah ya ce wa Annabi Isa (عليه السلام)ya kai Isa xan Maryam, ka tuna niimata a kanka, lokacin da na halicce ka ba da uba ba. Ka tuna niimata a kan mahaifiyarka Maryam (alaihas salam) yayin da na zave ta a kan sauran matan zamaninta. Ka tuna daga cikin abin da na yi maka niima da shi, yayin da na qarfafa ka da malaika Jibrilu (عليه السلام), kana yi wa mutane magana – alhali kana jariri – kana kiran su zuwa ga Allah, sannan kana musu magana kana dattijonka, kana faxa musu abin da na aiko ka da shi zuwa gare su. Daga cikin abin da na yi maka niimarsa na sanar da kai rubutu, na sanar da kai Attaura, wanda aka saukar wa Musa (صلى الله عليه وسلم) da Injilar da aka saukar maka, na sanar da kai sirrikan sharia da faidodinta da hikimominta. Daga cikin abin da na yi maka niimarsa kana suranta tsuntsu daga tavo, sannan ka yi busa a cikinsa, sai ya zama tsuntsu, kana warkar da wanda aka haifa yana makaho, kana warkar da mai kuturta, fatarsa ta yi kyau, kana raya matattu ta hanyar roqon Allah a kan ya raya su, dukkan waxannan abubuwa suna faruwa ne da izinina. Daga cikin niimar da na yi maka, na kare ka daga Bani Israil yayin da suka yi niyyar kasheka, lokacin da ka zo musu da muujizozi bayyanannu, suka kafirce da su, suka ce: babu abin da Isa ya zo da shi, sai sihiri bayananne.

وَإِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ءَأَنتَ قُلۡتَ لِلنَّاسِ ٱتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيۡنِ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالَ سُبۡحَٰنَكَمَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أَقُولَ مَا لَيۡسَ لِي بِحَقٍّۚ إِن كُنتُ قُلۡتُهُۥ فَقَدۡ عَلِمۡتَهُۥۚ تَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِي وَلَآ أَعۡلَمُ مَا فِينَفۡسِكَۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّـٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

الهوساوية | Hausa

Ka tuna ranar Alqiyama yayin da Allah zai ce – yana magana da Annabi Isa xan Maryam (عليه السلام) –: ya Isa xan Maryam, shin kai ne ka faxa wa mutane ku mayar da ni da mahaifiyata abubuwan bautawa koma bayan Allah?. Sai Annabi Isa ya bayar da amsa yana mai tsarkake Ubangijinsa ya ce: ba ya yiwuwa gare ni, in faxa musu wani abu sai gaskiya. Kuma da za a qaddara na faxi haka, da ka sani ya Allah, saboda babu abin da yake vuya gare ka, ka san abin da na voye a raina, amma ni ban san abin da ka voye a ranka ba. Kai kaxai ne ka san dukkan abin da ba ya nan, da dukkan abin da yake voye da wanda yake sarari.