وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Kuma ka ambaci labarin nana Maryam (alaihas salam) – ya kai wannan Manzo – a cikin Alqur‘anin da aka saukar maka, yayin da ta nesanci iyalinta, ta kaxaita a wani wuri can gabas da su.
فَٱتَّخَذَتۡ مِن دُونِهِمۡ حِجَابٗا فَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرٗا سَوِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai ta sanya shamaki tsakaninta da mutanenta, saboda kar su gan ta a lokacin da take ibada ga Ubangijinta, sai muka aiko mata da Mala‘ika Jibrilu (عليه السلام), ya fito mata da kamannin mutum mai cikakken halitta, sai ta ji tsoron kada dai yana neman ta da wani mummunan abu ne.
قَالَتۡ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Yayin da ta gan shi a kamannin cikakken mutum, yana fuskantar wurinta sai ta ce: “ina neman tsarin Allah mai rahama daga gare ka, kada ka yi mini wani mummunan abu – ya kai wannan mutum – idan har ka kasance kana tsoron Allah”.
قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Mala‘ika jibrilu (عليه السلام) ya ce: “ni ba mutum ba ne, ki sani ni xan aike ne daga Ubangijinki zuwa gare ki, domin na ba ki xa nagartacce, tsarkakakke”.
قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Nana Maryam tana cike da mamaki ta ce: “ta yaya zan samu xa, alhali ba ni da miji ko wani mutum da ya tava kusanta ta, kuma ni ba mazinaciya ba ce ballantana na haifi xan?”
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Mala‘ika Jibrilu (عليه السلام) ya ce mata: “lamarin haka yake, kamar yadda kika faxa, cewa xa namiji bai tava kusantar ki ba, kuma ke ba mazinaciya ba ce. Amma dai Ubangijinki ya ce: “halittar xa ba tare da uba ba, abu ne mai sauqi a wurina, kuma saboda xan da za a ba ki ya zama alama ga mutane bisa ikon Allah, kuma wata rahama ce ta musamman daga wurinmu zuwa gare ki, da duk wanda ya yi imani da shi. Kuma halittar wannan yaron naki qaddara ce daga wurin Allah abar zartarwa, rubutaccciya a cikin Lauhil-Mahfuz.
۞فَحَمَلَتۡهُ فَٱنتَبَذَتۡ بِهِۦ مَكَانٗا قَصِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai ta xauki cikinsa, bayan Mala’ika ya yi mata busa, ta nisanci mutanenta zuwa wani wuri mai nisa, inda babu mutane.
فَأَجَآءَهَا ٱلۡمَخَاضُ إِلَىٰ جِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ قَالَتۡ يَٰلَيۡتَنِي مِتُّ قَبۡلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسۡيٗا مَّنسِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai naquda ta kama ta, sai ta rave a jikin wani kututturen bishiyar dabino. Sai Nana Maryam (alaihas salam) ta ce: “kaicona! Ina ma dai na mutu kafin wannan rana, na kasance wani abun da ba a tuna da shi ba, saboda kada a yi mini mummunan zato”.
فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Annabi Isa (عليه السلام) ya kira ta daga qarqashin qafafuwanta ya ce mata: “kada ki yi baqin-ciki. Allah ya saka miki wani idon ruwa wanda za ki sha daga cikinsa”.
وَهُزِّيٓ إِلَيۡكِ بِجِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ تُسَٰقِطۡ عَلَيۡكِ رُطَبٗا جَنِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Kuma ki kama kututturen dabinon nan, ki jijjiga shi, nunannun ‘ya‘yan dabino, sababbin tsinkewa za su faxo miki.
فَكُلِي وَٱشۡرَبِي وَقَرِّي عَيۡنٗاۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدٗا فَقُولِيٓ إِنِّي نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَٰنِ صَوۡمٗا فَلَنۡ أُكَلِّمَٱلۡيَوۡمَ إِنسِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Ki ci ‘ya‘yan dabinon, kuma ki sha ruwan qoramar, sannan ki yi farin-ciki da jaririnki, kada ki yi baqin-ciki. Idan kuma kin ga wani mutum ya tambaye ki labarin jaririn, to , ki ce masa: “haqiqa na xora wa kaina cewa zan yi shiru, saboda neman yardar Ubangijina mai rahama, don haka yau ba zan yi magana da wani mutum ba”.
فَأَتَتۡ بِهِۦ قَوۡمَهَا تَحۡمِلُهُۥۖ قَالُواْ يَٰمَرۡيَمُ لَقَدۡ جِئۡتِ شَيۡـٔٗا فَرِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Nana Maryam ta zo da xanta wurin mutanenta, tana riqe da shi. Mutanenta cikin qyamata suka ce mata: “ya ke Maryam, lallai kin zo da wani abu, wanda muninsa ya girmama, kin zo da yaro ba tare da uba ba!”.
يَـٰٓأُخۡتَ هَٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمۡرَأَ سَوۡءٖ وَمَا كَانَتۡ أُمُّكِ بَغِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Ya ke wadda kika yi kama da Haruna a wajen ibada (wani mutumin kirki ne), babanki fa ba mazinaci ba ne, haka ma mahaifiyarki ba mazinaciya ba ce, ke daga tsarkakakken gida wanda aka san su da nagarta kike, don me za ki zo mana da yaro mara uba!”.
فَأَشَارَتۡ إِلَيۡهِۖ قَالُواْ كَيۡفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي ٱلۡمَهۡدِ صَبِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai ta yi nuni zuwa ga xanta Annabi Isa (عليه السلام) yana kan shimfixar haihuwa. Sai mutanenta cikin mamaki, suka ce mata: “yaya za mu yi magana da jariri wanda yake kan shimfixar haihuwa?”
قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا
الهوساوية | Hausa
Sai Annabi Isa (عليه السلام) ya ce: “lallai ni bawan Allah ne. Ya ba ni Injila kuma ya saka ni in zama xaya daga cikin annabawansa”.
وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا
الهوساوية | Hausa
“Kuma ya sanya ni mai yawan amfanarwa ga bayinsa a duk inda nake, kuma ya umarce ni da yin sallah, da bayar da zakka tsawon rayuwata”.
وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا
الهوساوية | Hausa
“Kuma ya sanya ni mai biyayya ga mahaifiyata, bai mayar da ni mai girman-kai ba, ko mai sabo wajen biyayyar Ubangiji ba”.
وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا
الهوساوية | Hausa
“Aminci daga sharrin shaixan da mataimakansa ya tabbata a kaina, ranar haihuwata, da ranar mutuwata, da ranar da za a tayar da ni da rai a gidan Alqiyama. Don haka shaixan ba zai iya fizga ta a waxannan matakai guda uku, masu ban tsoro ba”.
ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ قَوۡلَ ٱلۡحَقِّ ٱلَّذِي فِيهِ يَمۡتَرُونَ
الهوساوية | Hausa
Wanda aka siffanta da waxancan siffofin shi ne Annabi Isa xan Nana Maryam (عليهالسلام). Kuma wannan maganar ita ce zancen gaskiya dangane da shi, ba abin da vatattu masu shakku dangane da shi suke faxa kuma suke sava wa juna a ciki ba.
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
الهوساوية | Hausa
Sam-sam bai cancanta ga Allah ba ya xauki wani a matsayin xa. Ya xaukaka, ya tsarkaka daga yin haka. Duk lokacin da ya yi nufin wani abu, to kawai yana cewa abin ne “kasance”, sai ya kasance. Duk wanda ya kasance haka to ya fi qarfin a jingina masa xa.