التصنيفات
القرآن الكريم

المختصر في التفسير Hausa سورة [الأنبياء]

وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

الهوساوية | Hausa

Ya wannan Manzo ka ambaci qissar Nana Maryam (alaihas salam) wadda ta kare kanta daga zina, sai Allah Madaukakin Sarki ya aika mata da Malaika Jibrilu (عليهالسلام), ya yi mata busa, sai ta samu cikin Annabi Isa (عليه السلام). Kuma ita da xanta Annabi Isa sun kasance alamu ne ga mutane a bisa ikon Allah, da kuma cewa babu wani abin da zai gagare shi, ta yadda ya halicce shi ba tare da uba ba.