وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
الهوساوية | Hausa
Muka sanya Annabi Isa xan Nana Maryam (عليه السلام) da mahaifiyarsa Nana Maryam suka zama alama mai nuna ikonmu, domin ta xau cikinsa ba tare da mahaifi ba, kuma mun ba su mafaka a wani wuri mai tudu a bayan qasa, wanda yake madaidaici, kuma wurin ya dace da zama, a cikinsa akwai ruwa mai gudana, da kai kawo.