وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦوَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ
الهوساوية | Hausa
Allah ya bugawa (sanya wa) waxanda suka yi imani da Allah da manzanninsa misali da halin Nana Maryam ‘yar Imrana, wadda ta kiyaye farjinta daga aikata zina, sai Allah ya umarci mala’ika Jibrilu ya yi busa a jikinta, sai ta xauki cikin Annabi Isa da ikon Allah ba tare da uba ba, kuma ta gaskata da shari’o’in Allah, da littattafansa, waxanda ya saukar wa manzanninsa, kuma ta kasance daga cikin masu yi wa Allah xa’a, ta hanyar kamanta umarninsa, da nisantar abubuwan da ya hana.